Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pompeo Ya Isa Yankin Tsakiyar Turai


Pompeo (Hagu) bayan ya isa Czech Republic
Pompeo (Hagu) bayan ya isa Czech Republic

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ya kaddamar da ziyara na tsawon mako daya zuwa yankin tsakiyar Turai, in da a yau Talata ya yada zango a Janhuriyar Czech, inda zai gabatar da jawabi a taron cin abincin dare tare da Ministan harkokin waje Tomas Petricek. 

Ana sa ran Ponpeo zai kai ziyara wajen ajiye kayan tarihi domin tuna wa da rawar da Amurka ta taka wajen kwato wa nahiyar ‘yanci a locacin yakin duniya na biyu.

Ziyarar ta babban jami’in diflomasiyyar Amurka, na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Trump ke kokarin tinkarar Rasha da Chana a gasar da su ke yi ta fuskar tattalin arziki da siyasa a Turai.

Pompeo zai kai ziyara Prague da Pilsen dake Janhuriyar Czech; Ljubljana, Slovenia; Vienna, Austria; da kuma Warsaw, babban birnin kasar Poland, daga 11 zuwa 15 ga watan nan.

Zai kasance Sakataren Harkokin Wajen Amurka na farko tun 2011 da zai ziyarci Slovenia, inda zai sa hannu na hadin gwiwa akan fasahar sadarwa ta 5G, yayin da Amurka ke kokarin taka ma kasar Kwamines ta Chana, a yinkurinta na kutsawa cikin harkokin sadarwar zamani na yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG