Accessibility links

PSN sun bada bayani kan kanfanin magunguna na Jebu


Wata ma'aikaciyar kanfanin magunguna tana duban magani

Shugaban kanfanin magunguna na Nigeriya na sashin Jihar Lagos ya bayyana damuwarsa a bisa karuwar kanfanonin magani na jebu a jihar

PSN sun bada bayani kan kanfanin magunguna na Jebu

Shugaban kanfanin magunguna na Nigeriya, na sashin Jihar Lagos, Mr. Akintunde Obembe, ya bayyana damuwarsa a bisa karuwar kanfanonin magani na jebu a jihar.

Obembe, wanda yayi magana a taron shekara-shekara na 2012 na kungiyar kanfanonin magunguna na Nigeriya a jihar Lagos, ya shawarci gwamnatin tarayya ta karfafa kunguyoyin kasa domin suyi aiki bisa kan kanfanoni na magunguna da suke ta karuwa da saida magunguna na jebu.

Yace, an samukaruwar kanfanonin magunguna na jebu a cikin kasuwanni kuma dole a lura dasu ko kuma su zama wurin buyar masu saida magunguna na jebu a kasarmu Nigeriya.

Obembe yace idan wurin kanfanonin saida magunguna aka tsabtace su tawurin kunguyoyin da gwamnati ta kafa suyi haka, babu mai saida magunguna da zai iya ajiye ko kuma ya saida magungunan jebu ko kuma wadanda ba’a yarda da su ba ga al'umar kasa.

XS
SM
MD
LG