Accessibility links

Mutane biyu cikin uku na fuskantar barazanar kamuwa da cutar dundumi a Najeriya


Wadansu masu fama da cutar dundumi.

Ministan lafiya na Najeriya, Onyebuchi Chukwu yace mutane biyu cikin uku a kasar na fuskantar barazanar kamuwa da cutar dundumi.

Ministan lafiya na Najeriya, Onyebuchi Chukwu, ya bayyana cewa, mutane biyu cikin uku a kasar na fuskantar barazanar kamuwa da cutar dundumi.

Ministan ya bayyana haka ne a Abuja yayin wani taro da aka gudanar da nufin yaki da cutar da kuma zazzabin cizon sauro a Najeriya.

Najeriya ce kasa ta uku bayan Indiya da Indonesiya da aka fi fama da cutar dundumi da ake dauka da sauro ke yadawa.

Bincike na nuni da cewa sama da mutane miliyan dari suna fuskantar barazanar kamuwa da cutar yayinda a kalla jihohi 13 suke fama da cutar inda aka sami kimanin kashi 23 bisa dari yayinda sauran jihohin ke da a kalla kashi 10 bisa dari.

Ministan yace adadin mutanen da aka ba maganin cutar ya haura daga miliyan hudu da dubu dari bakwai a shekara ta dubu biyu da tara zuwa dubu goma a shekara ta dubu biyu da goma yayinda ake kan tattara rahoton shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

Bisa ga cewar ministan, sama da ma’aikatan lafiya 4,000 da ma’aiaktan sa kai tsakanin al’umma 50,000 suka sami horaswa domin rigakafi da jinyar cutar.

XS
SM
MD
LG