Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Ya Zargi Gwamnatin Obama da Shiryawa Sabuwar Gwamnatin Trump Zagon Kasa


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya zargi gwamnatin Amurka mai barin gado ta Barrack Obama da cewa tana kokarin yi wa sabuwar gwamnatin Donald Trump zagon kasa, ta hanyar baza jita-jita maras tushe gameda shi Trump din.

A wata hira da yayi da manema labarai jiya a birnin Moscow, shugaba Putin yace kasidun da aka baza a cikin makon jiya inda ake zargin Trump da wasu aiyukkan batsa a can Rasha,, duk wani bangare ne na kokarin da gwamnatin Amurka dake barin gado take yi na neman sa a rena kurar sabuwar gwamnatin ta Trump, a nuna kamar ba halatacciyar gwamnati bace.

Putin yace karya ce ake shatawa da rahottanin da ake yayatawa cewa wai Trump yazo Moscow a shekarar 2013, har yayi wata mu’amilar banza da karuwai a wata otel.

Putin yace masu baza irin wannan karyar sun ma fi karuwan rashin mutunci da rashin kima a idon kasashen duniya.

XS
SM
MD
LG