Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Qatar 2022: Argentina Ta Kai Zagayen Wasan Karshe


APTOPIX WCup Netherlands Argentina Soccer
APTOPIX WCup Netherlands Argentina Soccer

A ranar Lahadi za a buga wasan karshe a gasar ta cin kofin duniya wacce Qatar ke karbar bakuncinta.

Argentina ta doke Croatia da ci 3-0 a wasan zagayen dab da na karshe a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan Argentina Julian Alvarez ne ya zura kwallon farko a minti na 39 kafin a je hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kuma Alvarez ya kara wata kwallon a minti na 69.

Daga baya kuma Lionel Messi, ya kara wata kwallon da bugun fenariti.

Yanzu Argentina za ta jira wasa tsakanin Morocco da Faransa kafin ta wasan wanda za ta kara da shi a wasan na karshe.

A ranar Lahadi za a buga wasan karshe a gasar ta cin kofin duniya wacce Qatar ke karbar bakuncinta.

Sau biyu Argentina take lashe kofin gasar, wato a shekarar 1978 da 1986.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG