Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Kona Alkur'ani


Shugaban Amurka Barak Obama ya ce Paston nan ba-Amerike mai shirin kona Alkur’anai a harabar Majami’arsa da ke Florida ran 11 ga watan Satunba zai kasance wani mai taimaka wa al-Ka’ida ta sami karin mogoya baya ne kawai.

Shugaban Amurka Barak Obama ya ce Paston nan ba-Amerike mai shirin kona Alkur’anai a harabar Majami’arsa da ke Florida ran 11 ga watan Satunba zai kasance wani mai taimaka wa al-Ka’ida ta sami karin mogoya baya ne kawai.

A wata hira da shi da aka yada ta wani gidan talabijin da ke Amurka mai suna ABC yau Alhamis, Shugaba Obama ya ce niyyar Pastorn za ta jefa sojojin Amurka da ke a wurare irinsu Afghanistan cikin mummunan hadari. Kwamandojin soji ciki har da babban kwamandan soji a Afghanistan, Janar David Peytraeus da kuma babban kwamandan NATO, Anders Fogh Rasmussen, su ma sun yi kashedi.

Reverend Terry Jones ya gaya wa jaridar USA TODAY cewa zai sake salo idan aka tuntube shi daga Fadar White House ko Ma’aikatar Harkokin Waje ko Hedikwatan Tsaro ta Pentagon. Y ace ya zuwa yanzu dai ba a tuntube shi ba.

Jones, wanda ke jagorancin Majami’ar Dove World Outreach Centre mai mambobi 50, ya ce manufar shirinsa na cinna wuta kan abu mafi tsarki ga Musulmi ita ce aikawa da sako ga masu tsattsauran ra’ayin Islama.

Shugaba Obama ya bayyana shirin kona Alkur’ani mai Tsarkin da cewa fitina ce, to amman ya ce saidai Amurka na da wasu dokokin da ke bayar da yanci ga masu aika-aika irin wannan.

XS
SM
MD
LG