Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Shugaba Buhari da Atiku Abubakar Sun Banbanta Kan Harkokin tsaro


Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar
Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar

Shugaba mai ci Janar Muhammadu Buhari na jam’iyar APC, da kuma dan takarar babban jam’iyar hamayya PDP tsohon mataimakin Najeriya Alha Atiku Abubakar Wazirin Adamawa sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan harkokin tsaro.

A kashin farko na hirarsu da Sashen Hausa, ‘yan takarar shugaban kasar sun bayyana burinsu na ganin an kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya.

A bayaninsa, shugaba Muhammadu Buhari yace jam’iyarshi tayi yakin neman zabe inda ta zaga dukan jihohin Najeriya ta bayyana niyarta ta maida hankali kan batutuwa uku da suka hada da sha’anin tsaro, da tattalin arzikin kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Yace al’ummar arewa maso gabas zasu shaida cewa, gwamnatinsa ta taka rawar gani a wajen shawo kan hare haren kungiyar Boko Haram da suke kashe mutane da sunan addini.

Shugaba Buhari yace duk da yake ba a iya cimma burin murkushe kungiyar Boko Haram baki daya ba, an sani saukin hare harensu. Ya kuma bayyana cewa, aikin ‘yan sanda ne kula da harkokin tsaron cikin gida, sai dai yakan zama doke a tura sojoji idan ta baci kamar yadda ake yi a yaki da kungiyar Boko Haram.

Dangane da zargin cin hanci da rashawa a yaki da kungiyar Boko haran yace, abinda ya sani shine mayakan sama suke wannan yakin yayinda kungiyar take kuma amfani da kananan yara wajen kai hare hare.

A nashi bayanin, dan takarar jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar yace an sami sakaci a fannin harkokin tsaro da ya yi sanadin kashe ‘yan Najeriya da dama da ya hada da hari na baya bayan nan da aka kai inda aka kashe tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Alex Badeh da kuma a baya janar Idris Alkali.

Alhaji Atiku Abubakar yace jamai’in tsaro sun fi maida hankali kan harkokin siyasa a maimakon kare rayukan al’umma da tabbatar da tsaro. Ya kuma ce ya yarda da zargin da ake yi cewa, batun cin hanci da rashawa ne ya hana shawo kan kungiyar Boko Haram. Yace babu dalilin da yasa sojojin Najeriya da suka kware a yaki zasu kasa shawo kan ‘yan Boko Haram wadanda yace “yara” ne kanana da suka fara tada kayar baya da sanduna kawai.

Saurari Kashin farko na hirar Aliyu Mustpaha da ‘yan takarar.

Hira Da Shugaba Buhari da Alh Atiku PT1
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:55 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG