Mutumin farko da aka tambayi ra'ayinsa ya ce shi Donald Trump yake fatan ya zama shugaban kasar Amurka.
Yana fatar cewar idan Trump ya zama shugaban Amurka zai sa kasashen Afirka su samu 'yancin kansu su daina zubawa kasashen turai ido.
Mutum na biyu yana fatan Hillary Clinton ta ci zaben. Yace idan an duba can baya Hillary Clinton tayi aiki da Shugaba Obama kuma dukansu suna fahimtar da mutane.
Akan Donald Trump yace burinsa shi ne ya kori baki. Wani ma yace shi a gaskiya yana son Hillary Clinton taci zaben domin wai tayi aiki kuma tana da kwarewa. Tayi yawo wurare da yawa.
Amma Trump dan harka ne. Maganganunsa suna kawowa mutane fargaba tare da tsoratasu. Idan Trump ya ci zaben zai bata kasar. Da yaddar Allah Hillary Clinton zata ci zaben.
Ga karin bayani.