Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin 'Yan Najeriya Akan Nasarar Shiga Sambisa


Sambisa

‘Yan Najeriya, na ci gaba da bayana ra’ayinsu akan sanarwar rundunar Sojan Najeriya, na samun nasarar shiga dajin Sambisa, tare da kamo ‘yan kungiyar Boko Haram, da dama.

Tsohon mataimakin shugaban ‘yan Sandan Najeriya, Sanata Nuhu Aliyu, yace wannan babbar nasara ce ga ‘yan Najeriya, yana mai cewa yakamata a taya shugaban kasa murnar wannan gagarumin nasara.

Wani Malami a makarantar horar da Malamai dake Kontagora, Dr. Muhammad Imam, yace wannan nasara abin farin ciki ne a dai dai wannan lokaci wanda a cewarsa duk mai hankali mai kuma son Najeriya, wajibi ne yayi murna a cikin rayuwarsa da bayyanar da farin cikinsa a bisa wannan nasara.

Bayanai sun nuna cewa Sojojin sun ceto jama’a da dama daga ‘yan kungiyar ta Boko Haram, a cikin dajin na Sambisa.

Shugaban kungiyar Izala, ta najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau, yace akwai bukatar kulawa ta masamman ga yankin jihohin arewa maso gabashin Najeriya, da kungiyar ta Boko Haram ta daidaita.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG