Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

RAHOTO NA MUSAMMAN A KAN BOKO HARAM: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi - 'Tilas Mu Sake Ginawa' (Babi na 2)


Sace dalibai mata su fiye da 200 da ‘yan Boko Haram suka yi daga Chibok a ranar 14 Afrilu, ya janyo tofin Allah tsine daga fadin duniya. A bayansu, ‘yan Boko Haram sun kai hare-hare a kan malamai, kamar wadannan dake yin zanga-zanga a Maiduguri. (VOA/Ibra

Kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankula sun zamo ruwan dare a yankin arewa maso gabashin Najeriya a dalilin hare-haren ‘yan Boko Haram. A yayin da wannan tashin hankali ke bazuwa zuwa wasu sassan na Najeriya, har ma da makwabtanta, fargaba tana kara yawaita cewa watakila gwamnatin Najeriya ba ta san yadda zata takali wannan batu ba. Ko kuma tana kara rura wutar fitinar ne ma da kanta.

Idan mutum yaje shiga cikin Maiduguri, daya daga cikin abubuwan dake daukar hankalinsa shi ne taken jihar da aka rubuta a jikin wani allo: “The Home of Peace” watau Gida ko Cibiya ko Tungar Zaman lafiya. Daya daga cikin direbobin da muka yi hira da su, Yakubu Mohammed, yace kullum yana shige wannan allo idan ya debi fasinja daga Maiduguri zuwa Gamboru-Ngala dake bakin iyaka da Kamaru.

Wata rana a cikin watan Agustar 2013, ‘yan Boko Haram sun tare su a hanya, bayan da suka shige Dikwa kadan. Sun sanya masa hancin bindiga a fuska, suka fitar da fasinja uku cikin motar, suka harbe guda biyu har lahira a saboda sun ce ba Musulmi ba ne. Na ukun ya rantse musu shi Musulmi ne.

“Daga nan sai wani dan bindiga, yaro karami, kamar dan shekara 12 ma, ya kwace ma mutum na ukun wayoyinsa da kudin dake aljihunsa, suka ce masa ya koma cikin mota,” in ji Yakubu.

Direbobi, kamar wadannan da ake gani a tashar mota ta Mairi a Maiduguri, sun daina bin hanyoyi da dama a saboda fargabar 'yan Boko Haram dake tare hanyoyi su na kashe su. (VOA/Ibrahim Ahmed)

A jihohin da wannan fitina ta Boko Haram ta fi yin tsanani, watau Borno da Yobe da kuma Adamawa, harkokin kasuwanci sun tsaya cik a wasu sassan, wasu kuma rayuwarsu ma gaba daya ta tsaya.

A da, Borno ita ce cibiyar kasuwancin da ta hade Najeriya da kasashe kamar Kamaru, Chadi, Nijar, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Sudan da kuma kasashen Kwango guda biyu.

Wannan cinikayyar ta tsaya cik tun watannin baya, a saboda direbobi da ‘yan kasuwa su na fargabar bin hanyoyin. Shugaban majalisar ‘yan kasuwa ta Jihar Borno, Alhaji Rijiya Bama, ya ce, “A yanzu ba su zuwa a saboda yaran nan (‘yan Boko Haram) sun tare hanyoyi su na kashe direbobi su na kwashewa ko kona kayayyakinsu.”

A sassa da yawa na arewa maso gabashin Najeriya, musamman wadanda ke cikin dajin Sambisa ko makwabtaka da shi, da wuraren Bama, Konduga da Monguno da wasunsu, ayyukan noma sun tsaya a saboda ‘yan Boko Haram sun kori jama’a, ko kuma idan an shuka amfanin gonar ma zasu sace ko su lalata.

Duk da cewa yanzu ana cikin damina, akwai daruruwan motocin tarakta na noma da garma da wasu kayan aikin gona dake ajiye sun yi tsatsa a hedkwatar Hukumar Ayyukan Noman Zamani ta Jihar Borno dake Maiduguri. Masana su na kashedin cewa wannan na iya haddasa karancin abinci da tsadarsa.

Irin wannan mummunar fargaba, ba wai ta tsaya ga yankunan karkara ba ne kawai. Birnin Maiduguri, mai mutanen da suka zarce miliyan daya, kuma cibiyar ‘yan Boko Haram kafin a kore su, ya sha fuskantar hare-haren bam, ciki har da wani wanda aka kai ranar 14 ga watan Janairu.

(VOA Graphics)

A wannan rana, wani matashi mai suna Salihu yace yana gida ya ji karar tashin bam ta wajen inda mahaifinsa, Usman Masta mai Nama ke da tukuba a kusa da Fas Ofis. Wata mota cike da nakiya ta tashi, ta kashe mahaifinsa, ta raunata mutane masu yawa. Yanzu ya zamo maraya, kuma ya zamo shi ke rike da wannan tukuba da mahaifinsa ya bari.

“Aikin sayar da nama kawai na sani kuma na iya. Yanzu babu abinda zan yi, kamar zuwa makaranta ko wani abu. Wa zai kula da iyaye da sauran ‘yan’uwana” in ji shi?

A bayan shekara da shekaru ana ganin karuwar zub da jini, kungiyar Boko Haram ta yi kaurin suna a idon duniya a lokacin da mayakanta suka sace yara dalibai mata su fiye da 200 daga makarantar sakandare a garin Chibok na Jihar Borno. Kwanaki kadan a bayan sace daliban, shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fito cikin wani faifan bidiyo yana fadin cewa matan sun zamo bayinsu, kuma ba za a sako su ba sai idan gwamnati ta sako ‘yan’uwansu dake daure a gidajen wakafi.

Wata ‘yar shekara 17 daga cikin wadannan dalibai, wadda ta samu nasarar tserewa ita da wasu daliban biyu daga inda aka fara kai su bayan sace su, ta bayyanawa VOA yadda aka yi aka sace su, da yadda suka yi ta cire dankwalayensu su na jefarwa a kan hanya da gangan, cikin dare, bisa fatar cewa idan sojoji sun ji labarin an sace su, zasu zo su kwace su, kuma zasu yi ta ganin inda suka jefar da dankwalayen nasu su bi sawu.

Ta ce, “munyi ta cire dan kwalinmu muna jefarwa a kan hanya da yake dare ne, domin in soja suka ji labarin an sace mu, zasu iya bin sawu su zo su cece mu. Saboda haka muka yi ta jefar da dankwalinmu a kan hanya cikin dare.”

Taswirar yawan masu gudun hijira na cikin gida a jihohin da ake dokar-ta-baci, ya zuwa watan Maris na 2014. (VOA Graphics)

Duniya ta yi caa wajen nuna goyon bayanta ga wadannan ‘yan mata karkashin wani kyamfe mai suna #BringBackOurGirls, tare da kara matsin lamba a kan gwamnatin Jonathan ta yi wani abu domin kwato su. Wannan kyamfe ya samu goyon baya matuka daga manyan mutane a fadin duniya, cikinsu har da matar shugaban Amurka, Michelle Obama.

A yayin da wannan ke gudana kuwa, Maiduguri ta kara cika da tumbatsa da ‘yan gudun hijiran dake gudowa daga garuruwa da kauyukan dake kewaye a saboda hatsarin farmakin ‘yan Boko Haram. Garuruwa da kauyuka da yawa sun zamo babu ko mahaluki cikinsu, wasunsu ma an kona su gaba daya.

Karin Bayani akan Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>

XS
SM
MD
LG