Rahoton wanda aka kammala a karshen watan Agusta da ya gabata, na kunshe da wasu bayanan da asusun bayar da lamani na FMI ya tattara bayan binciken da aka gudanar a sassa daban daban na jamhuriyar Nijar, lamarin dake fayyace zahirin halin da ake ciki akan maganar yaki da cin hanci a wannan kasa.
A hirar su da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma, shugaban reshen transparency Malam Maman Wada ya kara haske akan wannan matsala, a bayanin sa.
Lokacin binciken na asusun IMF ya karkata akan kuri’ar jin ra’ayin jama’a game da yadda talakawa ke kallon batun cin hanci a Nijar.
Saboda haka zartar da doka akan dukkan wadanda aka tabbatar da samunsu da hannu a harkar cin hanci, ita kadai ce hanyar da za ta bada damar karya lagon masu aikata wannan haramtaciyar dabi’a.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.