Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Raila Odinga Da Magoya Bayansa Sun Yi Gangami


Shugaban 'yan adawa Raila Odinga a lokacin da yake jawabi ga dumbin magoya bayansa a birnin Nairobi. Ranar 13 ga watan Agusta, 2017.
Shugaban 'yan adawa Raila Odinga a lokacin da yake jawabi ga dumbin magoya bayansa a birnin Nairobi. Ranar 13 ga watan Agusta, 2017.

Abokin hamayyar shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya, Raila Odinga, ya yi wani gangami tare da wasu dumbin magoya bayansa kwanaki kadan bayan da ya sha kaye a zaben shugaban da aka yi.

Magoya bayan shugaban 'yan adawar Kenya, Raila Odinga, kusan 1,000 ne su ka taru daura da hanyar jirgin kasa da ke unguwar marasa galihu ta Kibera a Nairobi,babban birnin kasa a jiya Lahadi don sauraron jawabinsa, bayan galabar da abokin karawarsa, Uhuru Kenyatta ya yi kansa a zazzafan zaben Shugaban kasa da aka yi kwanan nan.

Amma Odinga da sauran mambobin kungiyar gamayyarsu ta NASA sun ce sace nasarar aka yi daga wurinsu, matsayin da su ka yi ta jaddadawa kenan ga magoya bayansu da ke cike da zakuwa.

Ya ce, "Mun zo nan ne don mu ce ku yi hakuri, ku yi hakuri, ku yi hakuri da abin da ya faru anan wurin jiya da kuma waccen ranar," a cewar Odinga.

Ya kuma kara da cewa, "Su na so su sace nasararmu, sannan kuma sun zo su kashe jama'armu. Wannan shi ake kira rashin bin doka."

To sai dai mai magana da yawun shugaban kasar Kenya Manoah Esipisu ya karyata wadannan zarge-zargen.

"Shugaban kasa ya ci wannan zaben kiri-kiri, masu saka ido da gida da na waje duk sun tabbatar da hakan," a cewar Esipisu.

Ya kara da cewa, mutane irinsu tsohon sakararen harkokin wajen Amurka John Kerry da Shugaba Thabo Mbeki na Afirka Ta Kudu, wadanda duk suka ce an yi zaben cikin adalci.


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG