Accessibility links

Ramadan: Marayu A Nijar Sun Samu Tallafi

  • Ibrahim Garba

Shugaba Muhammadou Issouhou na Nijar

Duk da rashin samun isassun kayan agaji, wata kungiyar ba da tallafi ga marasa galihu ta yinkuro don raba abin da ya samu ga marayu.

A cigaba da ayyukan alheri da ake yi albarkacin watan Ramadan, kungiyar taimakon marasa galihu da ke Maradi, ta kaddamar da rabon kayan tallafi irin abinci da kudade ga marayu. Shugaban kungiyar Malam Salisu Shu’aibu yay a ce kodayake bana ba su samu yadda su ke so ba, amma dai za a ba su adadin abinci kamar yadda aka saba, kudi ne kawai za a rage saboda kowa ya dan samu rabonsa.

Ya ce sun yi rajistan gidajen marayu wajen 700, amma saboda halin da ake ciki, rabinsu ne za su samu tallafi a yanzu. Daya rabin kuma sai dab da Sallah ko kuma bayan. Y ace kungiyar na samun tallafi daga daidaikun jama’a da kungiyoyi amma banda gwamnati.

Wasu daga cikin wadanda ke amfana da ayyukan wannan kungiyar sun yaba da tallafin da su ke samu. Wata mace mai kula da marayu uku ta ce ta samu marasa da hatsi da atanfa; kuma a baya ta samu kudi. Wata kuma ta ce kudi ta samu. Wata kuma cewa ta yi, “mu na samun kudi, mu na samun masara, mu na samun nama a lokacin Sallah – I na da marayu hudu, mata uku na miji daya.” Wakilinmu a Janhuriyar Nijar Shu’aibu Mani ne ya aiko da labarin.

XS
SM
MD
LG