Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

2023: Ranar 18 Ga Watan Fabrairu Za A Yi Zaben Shugaban Kasa - INEC


Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria)
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria)

"Hakan na nufin, saura shekara daya da wata tara da mako biyu da kwana shida ko kuma saura kwana 660 kenan a yi zabe daga yau.” In ji Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar zabe ta INEC mai zaman kanta a Najeriya, ta bayyana ranar da za a gudanar da babban zabe na gama-gari a shekarar 2023.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan, yayin wani taro da kwamitin kula da hukumar ta INEC a Majalisar Dattawa ya shirya na yini daya.

An hada taron ne don jin bahasi daga bakin hukumar kan kudurin dokar hukunta masu aikata laifukan zabe na 2021.

“Za a gudanar da babban zabe na gama-gari a ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023.” Farfesa Mahmood ya ce.

Lokacin da wata mata take kada kuri'a a Legas
Lokacin da wata mata take kada kuri'a a Legas

Ya kara da cewa, “hakan na nufin, saura shekara daya da wata tara da mako biyu da kwana shida ko kuma saura kwana 660 kenan a yi zabe daga yau.”

Shugaban hukumar ya kara da cewa, za su fitar da cikakken jadawalin yadda zaben zai gudana da zarar an kammala zaben Gwamna a jihar Anambra.

Za a yi zaben Anambarar ne a ranar 6 ga watan Nuwambar 2021 a cewar Farfesa Mahmood.

Dangane da taron, Farfesa Yakubu ya ce, babban kalubalen da hukumar ke fuskanta shi ne, jinkirin da ake samu wajen hukunta wadanda suka karya dokokin zabe.

Ya kara da cewa daga cikin kararrakin zaben 125 da aka gabatarwa hukumar, an samu nasarar yin hukunci akan guda 60 ciki har da na Akwa Ibom da aka yi a kwanan nan.

XS
SM
MD
LG