Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Alhamis Za a Fitar Da Tacaccen Rahoton Mueller - Ma'aikatar Shari'a

Babban Atoni-Janar din Amurka, William Barr

Shugaban na Amurka, ya fada ta kafar twitter cewa, da Mueller da Atoni-Janar din Amurka William Barr, bisa ga binciken da Mueller ya yi, sun yi ittifakin cewa babu wani hadin baki, kuma babu wani karen-tsaye ga shari’a da ya faru.

Ma’aikatar Shari’ar Amurka ta ce ranar Alhamis za ta saki tacaccen rahoton binciken na musamman na Robert Mueller, kan katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Shugaban kasar Amurka na 2016, da zummar ganin Donald Trump ya ci zaben Shugaban kasa.

Jiya Litinin Trump ya sake ikirarin cewa rahoton ya wanke shi daga duk wani rashin daidai a zaben, duk da yake, kamar sauran Amurkawa, shi ma ya na jiran cikakken bayanin binciken da aka kwashe watanni 22 ana yi..

Shugaban na Amurka, ya fada ta kafar twitter cewa, da Mueller da Atoni-Janar din Amurka William Barr, bisa ga binciken da Mueller ya yi, sun yi ittifakin cewa babu wani hadin baki, kuma babu wani karen-tsaye ga shari’a da ya faru.

Sannan Trump ya ce hasali ma, wadanda su ka aikata wadannan laifukan su ne abokiyar karawarsa, ‘yar takarar Democrat, Hillary Clinton, da kwamitin jam’iyyarta a matakin kasa, da kuma wadanda ya kira, “kazaman jami’an tsaro.” wanda da wannan suna na raini ya kan kira wasu tsoffin manyan jami’an tsaro.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG