Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Fadakar Da Jama'a Muhimmancin Bayar Da Gudunmawar Jini A Duniya


Ranar 14 ga watan junin kowace shekara rana ce da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ware domin fadakar da jama’a akan mahinmancin bada gudumuwar Jini domin ceton al’uma a sassa daban daban na Duniya. Daga Lagos Babangida Jibrin ya rubuto wanan labarin.

A sakon ta na bana domin wannan biki Shugabar Hukumar Lafiya Dr Magreth Chan, ta bayyana bada gudumawar jinni a matsayin wata kyauta da za a baiwa bil Adama, shima zai baiwa bi’adama dan uwansa domin ceton Rai. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewar ana samun gudumawar jini na kimanin Miliyan 108 a duk shekara, kuma kashi 50 cikin 100 na wannan gudumawa ana samun ta ne a kasashen da sukaci gaba, kasashen da kuma suke da kashi 20 cikin 100 na al’uman Duniya.

Sai dai abin takaici shine kamar yarda Hukumar Lafiyan tayi bayani she yadda kasashe masu taso basa samun gudumawar daya kamata duk kuwa da mahinmancin sa. Walau dai saboda da rashin ilmantarwa da rashin kayan aiki da kuma karancin malaman jinya ko kuma sauran naurorin gwajin jinin da ake bayarwa a asibitoci da ciboyoyin karban jini. Rahoton har ila yau yace kasashe 25 na Duniya basa iya gwajin jinni a sabili da rashin kayan aiki ko karancin jami’an lafiya.

To, ko ina mahinmancin bada gudumawar jinni? Dr Fumilyo Ajayi Likita ce a jihar Lagos, tace ko shakka bubu bada gudumawar jinni yana da mahinmaci kwarai da gaske don haka akwai bukatar jama’a su rinka bada jinni domin ceton rayukan jama’a. Don haka kawai bukatar wayar da kan jama’a domin bada gudumawar jini. Don haka ina bada shawara ga wayanda basa son bada gudumawar jinni dasu canza ra’ayinsu daga kin bayarwa zuwa bayarwa domin ceton al’umma.

To ko me jama’a zasu ce game da wannan rana da kuma bada gudumawar jinin? Malam Rabiu Lawal wani matashi ne daya sheda mani cewar shi kam bai taba bada gudumawar jini ba, amma kuma yasan mahinmancin bada gudumawar don haka yana ganin abune mai kyau da zai taimaka wajen ceton al’umma.

Shima a bangarensa Malam Ali ya ce shi kam ya taba bada gudumawar jini ga yayan cikin sa, don haka yana shawartar sauran jama’a sukasance masu bada gudumawar jini domin samun lada da ceton rayuka.

A duk shekara dai Gwamnatoci da sauran kungiyoyi ne ke gudanar da gangamin wayar da kan jama’a akan mahinmancin bada gudumawar Jini domin ceton al’umma.

Saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin daga Lagos.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG