Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Kawar Da Cin Zarafin Mata Ta Duniya


wata yar kasar Italiya a ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya.
wata yar kasar Italiya a ranar yaki da cin zarafin mata ta duniya.

Jiya Asabar dubban mutane ne a kasashen Turai su ka fito zanga-zanga domin karrama ranar kawar da cin zarafi ga mata ta duniya.

A birnin Paris, daruruwan mutane ne suka yi maci bayan da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sanar da shirinsa na shawo kan cin zarafin da ake yiwa mata a kasar. ya ce cikin shekarar 2016 mata 123 ne suka rasa rayukansu sanadiyar abokan zamansu ko kuma tsoffin abokan zamansu a Faransa.

Macron ya ce cikin shirye-shiryensa akwai karfafa doka kan wadanda suka ci zarafin mata, da karfafawa mata gwiwa wajen ‘daukar mataki idan hakan ya faru, da kuma kara ilimantarwa kan wannan batu.

A wata sanarwa da kungiyar Dare Feminism mai rajin kare ‘yancin mata ta fitar, ta ce shirin da Macron ya fitar abu ne masu kyau, amma dole sai ‘kara da kokari da kuma kudaden da za a tabbatar da su.

A fadin Duniya, an gudanar da zanga-zanga a kasashe irinsu Brazil da Mozambique da kuma Turkiyya.

A birnin Rome kuma, zanga-zangar ta hada da mutanen dake aiki a gidajen da aka ware domin matan da suka gujewa cin zarafi daga mazajensu ko kuma samarinsu.

Masu zanga-zangar sun yi kira ga ‘yan siyasar Italiya, da su mayar da hankali kan wannan batu, su kuma samar da karin kudaden da za a rika samar da mafaka ga matan da taimakawa kungiyoyin dake taimakawa mata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG