Accessibility links

Ran Lahadi Aka Yi Sallar Layya A Kasar Nijer

  • Halima Djimrao

Sallar Idi a Zinder, Damagaram, kasar Jamahuriyar Nijer.

'Yan kasar Nijer sun yi sallar Layya ranar lahadi.

Duk da cewa ranar Jumma'a aka yi hawan Arfa a kasar Saudiyya, a kasar jamahuriyar Nijer sai ranar lahadi aka yi sallar layya, ba ranar asabar ba kamar yadda akasarin kasashen Musulmi suka yi.

Majalisar Malaman Addinin Islama ta kasar Nijer ce ta ce lissafin da ta yi ya tabbatar ma ta a cewa ranar lahadi ya kamata a yi sallar layya a kasar ba ran asabar ba.

Sauram daidaikun jama'a kuma na bada hujja da cewa ran azumin kan, ran layyar ka.

An yi sallar layyar ce a kasar Nijer a daidai lokacin da ake ci gaba da juyayin mutuwar sojojin kara tara da aka kashe a kasar Mali.

Wakilin Sashen Hausa a Niamey, babban birnin kasar jamahuriyar Nijer Abdoulaye Mamane Amadou ne ya hada rahoton kuma ya aiko.

XS
SM
MD
LG