Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Tunawa da Yawan Jama'a A Duniya Ta Majalisar Dinkin Duniya


Matasa 'yan mata

Kowace ranar goma sha daya ta watan Yuli ce Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domn tunawa da ilahirin jama'ar duniya tare da mayar da hankali akan wani fannin rayuwar dan Adam.

A wannan shekarar ta tunwa da yawan jama'ar duniya Majalisar Dinkin Duniya ta maida hankali ne akan auren wuri ga yara mata da kan sa su zamo iyaye a lokacin da su ma suke bukatar kulawar nasu iyayen kana da azabtarwa da kuma nuna wariya ga jinsi mata lamuran da kan hanasu samun ilimin da ya kamata.

Rana wata yau wato, goma sha daya ga watan Yuli itace ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin tattauna makomar yawan jama'a a duniya.

Bikin na bana ya maida hankali ne akan lamuran da suka shafi 'ya'ya mata 'yan kasa da shekaru goma sha takwas wadanda suke fuskantar kalubalen rayuwa a sassa daban daban a duniya, kama daga auren wuri, hanasu sukunin samun ilimi ta hanyar ciresu daga makarantu gabanin kammalawa da kuma nuna wariya awasu lokutan baya ga musgunawa rayuwarsu.

Tauye 'yancin samun cikakken bayanai akan kiwon lafiya da 'yancin rayuwa na cikin tarin matsaloli da kalubale dake haifar da gibi ko kuma koma baya ga cigaban 'ya'ya mata a galibin sassan duniya.

Binciken masana ya nuna jimillar 'ya'ya mata miliyan 15 'yan kasa da shekaru 18 ne a ke yiwa aure a kowace shekara a sassa daban daban na duniya yayinda hukumar dake kula da yara ta majalisar dinkin duniya ko UNESCO ke cewa yara mata miliyan 31 ne basa iya zuwa makarantun firamare a kasashen duniya daban daban.

A wani hannun kuma adadin 'yan mata miliyan 60 ne basa samun sukunin shiga makarantu a matakin ilimi daban daban. Hukumar ta UNESCO ta cigaba da cewa akawai 'yan mata kusan miliyan biyar da rabi a Najeriya da basa zuwa makarantu. A Pakistan kuwa akwai fiye da miliyan uku. Habasha tana da miliyan guda da rabi.

Hukumar ta UNESCO tayi amannan cewa da a ce daukacin matan duniya zasu rika kaiwa ga matakin ilimin sakandare babu shakka da an kawar da kashi biyu bisa uku na matsalar auren wuri da ake fama da ita. Kazalika binciken yace mutuwar yara kanana zata ragu da abun da bai yi kasa da kashi 15 cikin 100 ba.

Da a ce duk matan duniy nada ilimin sakandare, da mutuwar yara ya ragu da kashi hamsin cikin dari.

Shugabannin gwamnati da na hukumomi masu zaman kansu da ma shugaban al'umma wajibi ne su tashi tsaye don kare hakkin 'yan mata musamman 'ya'yan talakawa wadanda talauci ke hanasu zuwa makaranta ko kuma ta hanyar azabtar dasu ta hanyar gargajiya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG