Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Tunawa Da Zaratan Sojojin Amurka Da Suka Rasu A Fagen Daga


Memorial Day
Memorial Day

Yayin da shugaba Donald Trump ke ziyara a Japan, mataimakinsa Mike Pence, ne ya ajiye furanni a gaban kabarin wani soja da ba’a san sunansa ba a makabartar da ke Arlington

Harkoki sun tsaya cik a yau Litinin a nan Amurka, domin a karrama sojojin kasar da suka mutu a fagen daga, yayin da ake hutun da Amurkawa suke wa lakabi da “Memorial Day” a turance.

Yayin da shugaban Donald Trump ke ziyarar a Japan, mataimakinsa Mike Pence, ne ya ajiye furanni a gaban kabarin wani soja da ba’a san sunansa ba a makabartar da ke Arlington wacce ke wajen birnin Washington.

Kafin ya dawo gida, ana sa ran shugaba Trump zai yi wani jawabi a gobe Talata ga dakarun Amurka a sasanin sojin ruwan kasar da ke Yokosuka a kasar ta Japan, inda zai magana akan hadin kan da ke tsakanin Japan da Amurka.

A yau Litinin, an tsara yin tarukan fareti a manya da kananan biranen Amurka, don tunawa da irin sadaukar da kai da dubban daruruwan dakarun kasar suka yi wajen samar da ‘yanci cikin shekaru 243 da kasar ta yi.

An kiyasi Amurkawa miliyan 1 da digo 1 suka mutu a sandiyar a yake -yake amma adadin mafi yawa da ya kusan rabin miliyan.. a karni na 19 suka mutu a lokacin yakin basasar kasar wanda aka yi tsakanin jihohin da ke arewaci da wadanda ke kudanci kan batun cinikayyar bayi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG