Accessibility links

Rasha Da China Sun Hau Kujerar Naki: Kuduri Kan Syria

  • Aliyu Imam

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Rasha da China sun hau kujerar naki kan kudurin Majalisar dinkin da ya kunshi barazanar azawa Syria takunkumi, idan shugabanta ya ci gaba da daukan munanan matakan murkushe ‘yan adawa a kasar.

Rasha da China sun hau kujerar naki kan kudurin Majalisar dinkin da ya kunshi barazanar azawa Syria takunkumi, idan shugabanta ya ci gaba da daukan munanan matakan murkushe ‘yan adawa a kasar. Wan matakin ya fusatar da Amurka da Turai.

Jakadiyar Amurka a Majalisar dinkin duniya Susan Rice, tace daftarin da Faransa, da Biritaniya da Jamus da Portugal suka rubuta, wasu kasashe sun gwammace sayarwa Syria makamai maimakon goyon bayan kudurin. Tace Washington tayi matukar bakin cikin ganin hakan, yayinda jakadan Faransa Gerard Araud, yace hawa kujerar nakin ba zai hana su ci gaba da daukan wan nan mataki da suka kudurta ba.

Madam Rice,da jakadan Ingila Mark Lyall sun fice daga dakin taron lokacinda jakadan Syria ya tashi yana Allah wadai kan kasahe dake neman a dauki mataki kan shugaba Bashar al-Assad.

Jakadan Rasha Vitaly Churkin yace Moscow tana adawa da takunkumi ganin galibin ‘yan Syria basa goyon bayan masu zanga zangar.

Har sau hudu kasashen turai da suka gabatar da kudurin suka yi masa kwaskwarima domin kaucewa wata ksa ta hau kujerar naki.Bayan kwaskwarimar kasashe tara suka goyi baya, kasashen hudu Lebanon, Afirka ta kudu, Brazil da India suka kauracewa jefa kuri’a.

Kudurin ya bukaci ba tareda bata lokaci a tsaida zubda jinni a Syria,da kuma kira na shimfida sabon shirin siyasa da bashi da alaka da tarzoma, tada hankali,tursawa jama’a, da kuma tsatsauran ra’ayi.

XS
SM
MD
LG