Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Na Kokarin Kawo Sulhu A Syria


Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da wakilin Siriya na musamman a Majalisar dinkin duniya Staffan de Mistura

Duk da korafin da 'yan adawar Siriya suka yi tare da cewa ba zasu halarci taron na Sochi ba, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov yace su na samun goyon bayan al'ummar Siriya sosai kan taron zaman sulhun da suka shirya.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fada yau Laraba cewa, shawarwarin sulhu kan rikicin Syria da Rasha zata jagoranta a wata mai zuwa a Sochi, ta sami gagarumin goyon baya daga jama’ar Siriya, kuma ana sa ran zaman zai kasance ginshikin shirin samar da zaman lafiyar da Majalisar Dinkin Duniya zata shiga Tsakani kan rikicin kasar.

Kalaman Lavrov na zuwa ne bayan da wata hadakar kungiyoyin ‘yan tawayen Siriya su 40 suka ce Rasha na kokari ne ta kaucewa shirin samar da zaman lafiya na MDD kuma ba za su halarci ganawar da za’a yi a Sochi ba.

‘Yan tawayen sun ce Rasha na nema ne su yi watsi da bukatun su na cewa shugaba Bashir al-Assad ya sauka daga kan mulki.

’Yan tawayen sun ce duk kasa ko hukumar da zata shiga tsakani a ganawar ta samar da zaman lafiya dole ne ta kasance wadda bata da bangare mai kamanta gaskiya kuma. Suka kuma ce Rasha, a matsayin babbar kasar dake kawance da Syria, ba ta cancanta ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG