Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Leken Asiri Na Amurka-Putin Da Gwamnatin Rasha, Sun Goyi Bayan Trump.


Darektan hukumomin leken asiri na Amurka James Clapper.
Darektan hukumomin leken asiri na Amurka James Clapper.

Hakan yana kunshe cikin wani rahoton sirri da aka bayyana ranar Jumma'a.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya kuduri anniyar gurgunta zaben Amurka na bara, ya muzanta tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, "a wani mataki da ba'a taba ganin irinsa ba," daga bisani ya tsaida shawarar taimakawa Donald Trump, kamar yadda aka gani a bayanan sirri da hukumomin leken asirin Amurka suka fitar.

"Haka nan mun ayyana cewa, shugaba Putin da gwamnatin Rasha sun fi son shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump," rahoton ya ci gaba da cewa, Putin da gwamnatin Rasha, sunyi kokarin su taimkawa shugaban Amurka mai jiran gado ta inda duk suka sami damar yin haka."

Manyan hukumomin leken asiri na Amurka uku ne suka saki rahoton, sa'o'i bayanda shugabannin hukumomin suka yi bayanin siri ga shugaban na Amurka mai jiran gado Donald Trump a birnin New York. Shugaban Amurka mai barin gado Barack Obama, wanda ya bada umarnin a gudanar da binciken,ranar Alhamis ne aka yi masa bayani kan sakamkaon binciken.

A cikin rahoton, duka hukumomin CIA da FBI suka ce suna da cikakken kwarin guiwa kan sakamkon biciken da suka gudanar. Hukumar ta uku, mai-leken asiri ta na'urori da ake kira NSA, ta ce ta goyi bayan matsayar takwarorinta biyu,amma kwaringuiwarta kan sakamkon binciken bai matsyar da takwarorin nata biyu suka bayyana ba.

Trump ya kira bayanai da aka gabatar masa a zaman mai ma'ana.Amma a cikin wata sanarwa da ya fitar daga bisani yace duk wani kokari da Rasha ko wasu kasashe suka na yin katsalandan cikin zaben Amurka daga karshe kokarinsu bashi da wani tasiri kan makomar zaben da aka yi cikin wata Nuwamban bara.

XS
SM
MD
LG