Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Kammala Jigilar Makaman Nukiliya Zuwa Makwabciyarta Belarus


Makamin Nukiya mai cin gajeren zango.
Makamin Nukiya mai cin gajeren zango.

Shugaban kasar Belarus ya ce Rasha ta kammala jigilar makaman nukiliya da take yi zuwa kasarsa, matakin da ya haifar da kakkausar suka a makwabciyarta Poland da sauran kasashen yankin.

Shugaban kasar Alexander Lukashenko, ya bayyana haka ne a taron kungiyar tattalin arziki karkashin jagorancin Rasha a birnin St. Petersburg, cewa tun watan Oktoba aka kammala jigilar makaman amma bai yi karin bayani kan yawansu da kuma inda aka ajiyesu ba.

Makaman nukiliyan wadanda aka yi niyyar amfani da su a fagen fama, masu cin gajeran zango ne kuma tasirinsu bai kai na sauran kananan ba, idan aka kwatanta da manyan makaman nukiliya masu karfi wadanda ke cin dogon zango.

Rasha ta ce za ta ci gaba da kula da makaman da ta tura zuwa Belarus.

Lukashenko ya ce karbar makaman Nukiliyar Rasha a cikin kasarsa na nufin dakile ta'asar Poland, wadda mamba ce ta kungiyar tsaro ta NATO.

Kasar Poland dai na bai wa makwabciyarta Ukraine goyon bayan soji da na jin-kai da na siyasa a gwagwarmayar da take yi da mamayar Rasha, kuma tana taka rawa a takunkumin kasa da kasa kan Rasha da Belarus.

Dakarun Rasha da ke zaune a Belarus sun mamaye Ukraine daga arewacin kasar a farkon yakin, amma ba a san ko sojojin Belarus sun saka hannu ba.

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG