Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha ta kawo shawarar tsagaita wuta a yakin Siriya


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Kasar Rasha na kawo shawarar tsagaita wuta a Siriya, yayinda ministocin harkokin waje ke gudanar da wani taro a birnin Munich don neman hanyar da za’a kawo karshen mummunann yakin basasar da ya jefa kasar ta larabawa cikin bala’i.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Gennady Gatilov, ne ya bada wannan Shawarar yana kuma kira akan ta fara aiki daga ranar daya ga watan 3. Kasar Amurka kuma ta ce a’a, kamata yayi tsagaita wutar ta fara aiki ba tare da bata lokaci ba don a samu a tura da taimakon agaji a biranen Siriya da aka mamaye.

Tashin hankalin da aka kwashe shekaru 5 ana yi, wanda janyo adawa tsakanin shugaba Assad da ‘yan tawayen kasar da ke neman hambare gwamnatin sa, ya haddasa mutuwar mutane fiye da dubu dari biyu da hamsin kuma ya zamo rikin agajin jinkai mafi muni da aka taba gani a duniya cikin shekarun da suka wuce.

Rasha ta kaddamar da hare-hare ta sama don mara wa gwamnatin shugaba Assad baya, abinda ta ce ta yi ne da niyyar yaki da ‘yan kungiyar ISIS da su ka yi yawa a Siriya. Amma Amurka da wasu kasashen yammacin duniya sun ce yawancin hare-haren ta sama sun auna kungiyoyin da ke adawa da shugaba Assad ne kawai.

XS
SM
MD
LG