Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Diflomasiyya: Rasha Ta Kira Jakadun Wasu Kasashe da Ke Birnin Masko (Moscow)


Trump da Putin

A cigaba da dambarwar diflomasiyya da ake yi tsakanin Amurka da wasu kasashe 20 a gefe guda da kuma Rasha a daya gefen, Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha ta kira jakadun wasu kasashen don bayyana rashin jin dadinta.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta kira manyan jami’an diflomasiyyar kasashen da su ka kori jami’an diflomasiyyar Rasha don ta mika masu takardar nuna rashin jin dadinta ta kuma bayyana masu matakan ramuwar gayyar da za ta dauka.

An ga Jakadan kasar Jamus na barin Ma’aikatar ta Harkokin Wajen Rasha a yau dinnan Jumma’a, a yayin da aka kuma ga jakadun kasashen Netherlands da Ukraine da Faransa da Italiya da Poland na isowa.

Jiya Alhamis Amurka ta ce Rasha ba ta da hujjar daukar wani matakin ramuwar gayya ta wajen korar jami’an diflomasiyyar Amurka.

Daga bisani a jiya Alhamis din Fadar Shugaban Amurka ta White House ta fitar da wata dakartar bayani, inda ta ke cewa matakin da Rasha ta dauka ya dada sukurkuntar da dangantaka tsakanin Amurka da Rasha.

Amurka da sauran kasashe sama da 20 sun soke takardun aikin jami’an diflomasiyyar Rasha, wadanda kasashen su ka zarga da gudanar da ayyukan leken asiri, bayan da aka zargi Rashar da kai harin guba kan wani tsohon dan leken asirinta Sergei Skripal da diyarsa Yulia, a farkon wannan watan a Salisbury.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG