Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Sanar Da Mallakar Sabbin Makamai Masu Linzami


Shugaban Rasha, Vladimir Putin

Rasha ta bayyana mallakar wasu sabbin makamai na nukiliya da na linzami yayin da shugaban kasar yake bayyana halin da kasa ke ciki ga 'yan majalisar dokokin kasar.

A yau Alhamis Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce dakarun kasar sun yi gwajin sabbin makaman nukiliya, ciki har da wani makami mai linzami da ke iya tafiya mara iyaka, wanda kuma zai iya kauce wa duk wani makarin makami mai linzami.

Putin ya bayyana hakan ne, yayin jawabinsa ga ‘yan majalisar dokokin kasar, kan halin da kasa ke ciki, yayin da kasar ke shirin gudanar da zabe a ranar 18 ga watan Maris.

Baya ga wannan nau’in makami mai linzami, shugaba Putin ya ce, Rasha ta kera wani sabon makami mai linzami, wanda zai iya ratsa nahiyoyi da ake wa lakabi da “Sarmat”, wanda ke iya tafiyar dogon zango dauke da rassa, fiye da wanda kasar ta kera a baya.

“Sarmat wani makami ne mai karfin gaske, kuma saboda irin suffufinsa, yana da karfin da zai iya zama cikas ga duk wani makarin makami mai linzami.” Inji Putin.

Baya ga batun karfin sojin Rasha, Shugaba Putin, ya saka wa’adin da zai rage matsalar talauci a kasar a wa’adinsa na biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG