Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Za Ta Koma Kera Makaman Nukiliya

Yayin da shugaba Putin (dama) ke tattaunawa da ministan harkokin wajen Rasha, Sergie Lavrov (hagu)
Yayin da shugaba Putin (dama) ke tattaunawa da ministan harkokin wajen Rasha, Sergie Lavrov (hagu)

A wani jawabi da ya yi ta kafar talbijin yayin wani taro da ya yi da ministocin harkokin waje, da manyan kwamandojin kasar, Putin ya ce “takwarorinmu na Amurka sun ayyana cewa sun janye daga wannan yarjejeniya da aka cimma, saboda haka, mu ma mun janye.”

Shugaban Rasha, Vladmir Putin, ya jingine matsayar da aka cimma ta dakile kera makaman nukiliya, wacce aka rattaba hannun akan ta tun a lokacin ana yakin cacar baka, a matsayin martani ga matakin da Amurka ta dauka a jiya Juma’a.

A wani jawabi da ya yi ta kafar talbijin yayin wani taro da ya yi da ministocin harkokin waje, da manyan kwamandojin kasar, Putin ya ce “takwarorinmu na Amurka sun ayyana cewa sun janye daga wannan yarjejeniya da aka cimma, saboda haka, mu ma mun janye.”

Ita dai Amurka ta sha alwashin za ta janye kwatakwata daga wannan matsayar da aka cimma, ta dakatar da kera makaman na nukiliya nan da watannin shida masu zuwa, muddin hukumomin Moscow ba su kawo karshen aikace-aikacen da suke yi ba, wadanda Amurkan ta ce sun saba wannan yarjejeniya wacce aka kulla a shekarar 1987.

Shugaba Putin ya ce, Rasha za ta fara wani gagarumin aikin kera makamai masu linzami, sannan ya bai wa ministocinsa umurnin cewa kada su fara wani shirin sasantawa da hukumomin Washington.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG