Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Zata Fuskanci Barazana A Damascus


Vladimir Putin

Rasha tace shawarar da Amurka ta yanke a kwanan nan na sausauta kayade baiwa 'yan tawayen Syria makamai, mataki ne na tsokana da zai dagulawa muradun sojojin Rasha da wasu kasashe a Syria.

Jiya Talata mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Maria Zakharova ta cacaki canjin manufar, tana mai fadawa kamfanin dilancin labarun Reuters cewa an rubuta yiwuwar baiwa 'yan tawaye makamai cikin sabuwar dokar.

Tace kai tsaye mayakan saman Rasha da sojojin ta da ofishin jakdancin Rasha a birnin Damascus zasu fuskanci barazana, kuma akwai yiwuwar makaman sun fada hannun ‘yan Jihadi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG