Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Aikin Yi Yasa Na Shiga Fashi Da Makami


Hoton masu satar mutane

Rundunar 'yan sandan NIgeria tayi nasarar kame wasu 'yan fashin da makami dake fashi tsakanin Abuja da Kaduna

Rundunar ‘yan sanda Najerya ta musamman dake karkashin ofishin sifeta janar na ‘yan sanda ta sami nasarar damke wani jagoran masu garkuwa da mutane da kuma wadanda ke samar masu da bindigogi da harsasai.

Da yake bayani ga manema labarai a ofishin ‘yan sanda, daya daga cikin mutanen da suka shiga hannu ya bayyana cewa, rashin aikinyi ya sa ya shiga satar shanu kafin ya gamu da wani wanda ya nuna masa garkuwa da mutane yafi riba, wadda a fitar farko ya tashi da naira dubu hamsin akasin dubu goma zuwa sha biyar da yake samu ta hanyar satar shanu.

Banda masu garkuwa da jama’a domin neman fansa, rundunar ta kuma kama wadanda suke samar masu da makamai da kuma harsasai, da suka hada da wani dattijo dan shekara saba’in da tara, wanda ya bayyanawa Sashen Hausa cewa, shi tsohon maharbi ne, ya kuma shiga sana’ar saida bindigogi ne da yake samu daga hannun wani da yace yana samu a bakin ruwa inda ake sauke kaya.

Daga cikin wadanda aka kama akwai wani mutum da a ranar aka ce ya sayar da harsasai dubu daya ga masu satar mutane.

Su dai wadannan barayin suna aiwatar da wannan mummunar sanaar tasu ce akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rundunar ‘yan sandar tace ba zatayi kasa a gwiwa ba har sai ta murkushe masu wannan mummunar sana'ar cikin kasa.

Ga Hassan Maina Kaina da Karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG