Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Halartar Lauya A Kotu Ya Kawo Cikas Ga Gurfanar Da Yahaya Bello

Yahaya Bello a cikin Kotu
Yahaya Bello a cikin Kotu

Yahaya Bello wanda ya yiwa kotun jawabi da kansa, ya shaidawa mai shari’a Emeka Nwite cewa an sanar da shi game da batun gurfanarwar ne a kurarren lokaci a jiya Alhamis 28 ga watan Nuwamban da muke ciki don haka bai samu damar sanar da lauyoyinsa ba.

Gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello gaban babbar kotun tarayya dake Abuja ya gamu da cikas sakamakon rashin bayyanar lauyansa.

Hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ce ta gurfanar da tsohon gwamnan a bisa tuhume-tuhume 19 dake da nasaba da halasta kudaden haram har Naira biliyan 80.2.

A yayin zaman kotun na yau, lauyan hukumar EFCC Kemi Pinhero ta gabatar da bukatar karantawa wanda ake kara tuhumar da ake yi masa tare da neman jin ra’ayinsa akai

Yahaya Bello wanda ya yiwa kotun jawabi da kansa, ya shaidawa mai shari’a Emeka Nwite cewa an sanar da shi game da batun gurfanarwar ne a kurarren lokaci a jiya Alhamis 28 ga watan Nuwamban da muke ciki don haka bai samu damar sanar da lauyoyinsa ba.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG