Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Iskar Shaka Na Kashe 'Yan Gudun Hijrar Afirka Zuwa Turai


Wasu Bakin Haure a Jirgin Ruwa Bayan Cetarsu Daga Nutsewa
Wasu Bakin Haure a Jirgin Ruwa Bayan Cetarsu Daga Nutsewa

Ana ci gaba da samun karuwar masu haurawa zuwa Turai daga kasashen Afirka a yayi da rashin isasshiyar iskar shaka a jiragen ruwansu take hallaka su.

Kungiyar duniya game da ‘yan gudun hijira ta duniya ta bada rahoton cewa, ana fa samun karuwar masu kokarin tarar aradu da ka don haurawa Turai daga kasashen yankunan Saharar Afirka.

Ta inda suke ratsawa ta cikin teku a manyan kwale-kwale da ke fuskantar hatsarin salwantar da rayuwarsu, bayan sun baro kan gabar tukun daga kasar Liya a kokarin tsallakewa zuwa Italiya.

Lisa Schlein ta kungiyar ‘yan gudun hijirar ta bayyana cewa, a ‘yan makonnin nan an ceci mutane da suka kusa halaka a cikin teku sama da 1000 zuwa wasu tashoshin jiragen ruwan Italiya.

Rahoton ya nuna cewa mafi yawancin mutuwar da ake yi tana faruwa ne sakamakon sikewar numfashi saboda karancin iskar da dandazon jama’ar da ke makare a jiragen ruwan za su shaka.

XS
SM
MD
LG