Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tabbatar da Onnonghen Alkalin Alkalan Najeriya Ya Damu 'Yan Cross Rivers dake Majalisar Dattawa


Yayinda shugaban Najeriya yake rantsar da Walter Onnonghen a matsayin mukaddashin alkalin alkalan Najeriya a Abuja

Kusan watanni uku ke nan da Shugaba Muhammad Buhari ya rantsar da Walter Onnonghen a matsayin mukaddashin alkalin alkalan Najeriya amma rashin tabbatar dashi akan mukamin ya sa kungiyar 'yan jihar Cross Rivers, jihar asalinsa dake Majalisar Dattawa damuwa.

Bisa doka wa'adin wata uku ake ba wanda aka ba mukamin na rikon kwarya idan kuma ba'a tabbatar masa da mukamin ba dole ne ya sauka bayan wata ukun.

Yanzu dai wa'adin Justice Walter Onnonghen wanda ya fito daga jihar Cross Rivers zai cika wannan watan.

A wani taron manema labarai da kungiyar ta kira ta bayyana irin cecekuce dake tasowa akan tsawon lokaci da Walter Onnonghen ya kwasa yana zaman rikon kwarya. Kungiyar tace ire-iren maganganun dake fitowa ka iya jawo rarrabuwan kawuna idan fadar shugaban kasa bata dauki mataki cikin gaggawa ba.

Sanata John Eno shi ne ya shugabanci kungiyar 'yan Cross Rivers din inda yace suna samun bayanai dake nuni cewa akwai wasu dalilai da suka sa har yanzu ba'a ba Walter Onnonghen mukamin alkalin alkalan kasar ba, wadanda suka jibanci kabilanci da wariya. Yace akan haka ne suke kira ga shugaban kasa da ya gaggauta daukan mataki kafin watanni uku su cika.

Walter Onnonghen mukaddashin alkalin alkalan Najeriya
Walter Onnonghen mukaddashin alkalin alkalan Najeriya

Mai Nasara Kogo Ibrahim masani akan kundun tsarin mulkin kasa yace akwai bangaren sashin mulkin Najeriya da yace idan an ba mutum mukamin mukaddashin alkalin alkalan Najeriya yayi wata uku ba'a tabbatar dashi ba ba za'a kara masa wasu kwanaki ba.

A bangaren Majalisar Wakilai kuma Abdullahi Umar Majikira daga jihar Kebbi yace ba mukamin alkalin alkalai kadai ba ne ba'a nada ba. Akwai wasu hukumomi da dama da ba'a nadasu ba.

Mai shari'a Walter Onnonghen zai cika watanni uku akan mukamin mukaddashin alkalin alkalan Najeriya 10 ga wannan watan na Fabrairu.

Ga Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG