Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tsabtace Muhalli Yana Kawo Zazzabin Cizon Sauro


Hoton sauro

Shugaban asibitin Maisamari dake garin Maradi Ibrahim Sabbi ya bayyana cewa rashin tsabta yana iya sa mutane su kamu da zazzabin cizon sauro wanda yafi kama kananan yara, kamar jarirai zuwa shekaru biyar.

Shugaban asibitin Maisamari dake garin Maradi Ibrahim Sabbi ya bayyana cewa rashin tsabta yana iya sa mutane su kamu da zazzabin cizon sauro wanda yafi kama kananan yara, kamar jarirai zuwa shekaru biyar. Yace a cikin kashi dari da suke kamuwa da zazzabin cizon sauro, wajen kashe tamanin duka yara ne.

Haka kuma mata masu juna biyu suna kamuwa da zazzabin cizon sauro, ya bayyana cewa suna ba masu fama da zazzabin cizon sauro magani kuma babu wanda ya rasa ranshi daga cikin wadanda suka je asibiti domin neman magani.

Likitan yace ya kamata mutane su kula da tsabta su kuma kula da kwana a cikin gidan sauro. Yace da idan an ba mata gidan sauro suna saidawa amma yanzu da wuya kaje cikin kasuwa ka same shi, sun gane muhimmancin wannan gidan sauron.

Wani kuma da aka yi hira da shi yace mata suna bari sai sauro ya rika cizon yara kafin su kaisu su kwantar da su a cikin gidan sauro abinda ya sa yaran suke kama zazzabin cizon sauro

Wakilin Sashen Hausa Sha’aibu Mani ya aiko da rahoton.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG