Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tsaro Ya Haifar Da Zanga-zanga a Jihar Adamawa


ZANGA ZANGAR ADAMAWA
ZANGA ZANGAR ADAMAWA

An gudanar da zanga-zangar lumana ranar Talata a jihar Adamawa, kan karuwar rashin tsaro da garkuwa da mutane, inda masu zanga-zangar su ka yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kawo musu dauki.

Masu zanga zangar sun kafa shingaye a manyan hanyoyin dake shiga fadar gwamnatin jihar ta Yola, kana sun rike kwalaye masu rubutu kamar hala “ Satar mutane ya wuce gona da iri a Girei”, Ya kamata gwamnatin ta kawo mana dauki” da kuma “ A bamu tsaro a Girei”.

A cikin wannan lokaci, an samu batun yawan satar mutane a wasu garuruwan jihar Adamawa, lamarin dake hana mazauna yakunan barci.

Wannan matsala ta garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na hana jama'a barci a yanzu musamman a arewacin Najeriya.

Yankin Girei, a jihar Adamawa na cikin yankunan da lamarin ya munana, batun da ya kai al'umomin yankin kafa kungiyoyin Sakai na matasa, da har suka samu nasarar cafke wasu da ake zargi, kuma suka danka su ga ‘yan sanda, amma wata sabuwa ta kunno da har ta kai jama'ar gari sun fusata tare da gudanar da zanga-zanga tare da rufe babbar hanyar garin da ya hade garin da fadar jihar.

Sakamakon wannan takaddamar ne ya sa shugaban karamar hukumar da jami'in ‘yan sandan garin da kuma wasu shugabanin al'umma garzayawa zuwa shedikwatar ‘yan sandan jihar Adamawan, inda suka gana da kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Audu Madaki.

Kamar yadda bincike ke nunawa baya ga matsalar Boko Haram, yanzu haka ba wata matsalar dake neman gagaran kundila kamar ta masu garkuwar.

Domin karin bayani saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz daga birnin Yola:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG