Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mallam Adamu Ciroma Ya Rasu


Adamu Ciroma
Adamu Ciroma

Allah ya yi wa tsohon shugaban babban bankin Najeriya, minista, kuma daya daga cikin dattijan kasa, Mallam Adamu Ciroma rasuwa yau Alhamis yana mai shekaru 83 da haihuwa a asibitin Turkawa da ke Abuja.

Marigayi Madakin Fika, Mallam Adamu Ciroma wanda haifaffen garin Potiskum ne da ke Jihar Yobe, ya rasu yau alhamis bayan rashin lafiya yana mai shekaru 83 da haihuwa.

Ciroma ya rike mukamai da dama da suka hada da gwamnan babban bankin Najeriya, da minista har sau uku na kudi da masana’antu da kuma na harkokin Noma. Sannan ya taba tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 1979 karkashin Jam’iyyar NPN, yana kuma daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP.

A baya ya taba aiki da kamfanin Jaridar Arewacin Najeriya wato 'New Nigerian Newspaper' kasancewar digirinsa na biyu a fannin aikin jarida ne daga Kwalejin Koyon Aikin Jarida ta Jami'ar Columbia da ke birnin Newa York a Amurka.

Amma kafin sannan ya dan yi aiki a Jiharsa ta Bauchi bayan ya kammala digirinsa na farko a fannin kididdigar kudi daga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Aminin marigayin, kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Yobe, Alhaji Baba Ba’abba ya bayyana cewa rayuwarsa tun yana karamin ma’aikaci a lokacin gwamnatin Sardauna, mutum ne da aka sani da magana daya.

“Ba ya magana da ganganci, abin da ya fada din nan shine karshe. Kuma bisa ga shaidun da ya samu tun daga kan wandanda ya yi aiki da su, da ma wadanda bai yi aiki da su ba,” inji Ba’abba.

Ba’abba ya bayyana cewa a kwanan baya, shugaban kasa ma ya jinjina masa cewa a lokacin da yayi canjin gwamnati, yana daga cikin wadanda suka ba shi sha’awa saboda yadda suka tafiyar da ayyukansu, inda suka gama lafiya ba su cuci kowa ba kuma ba su bata sunansu ba.

A wata sanarwar da aka fitar yau, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikin rashin da aka yi kuma yana mika ta'aziyyarsa ga iyalansa. Ya kuma yabi hidimar da ya yiwa Najeriya domin tabbatar da hadin kai, da ci gaba, da kuma samun zaman lafiya a kasar.

Buhari ya tabbatar za a karrama tsohon gwamnan babban bankin saboda gudummuwar da ya bayar wajen habaka tsarin dimukuradiyya a Najeriya, kuma yace, tarihin abubuwan kirki da Mallam yayi, ya zamanto abin koyi ga ‘yan siyasa da ke neman yi wa kasa hidima domin kyautata makomar kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG