Accessibility links

Rawar ‘Yan Jarida akan tashe-tashen hankula


Wasu da wani rikici a taba ritsawa da su a baya

An yi taron bitar karawa juna sani na ‘yan jarida a Jos da ke jihar Filato game da yadda ya kamata su taka rawa wajen dakile wutar rikici.

Taron da cibiyar koyar da dabarun mulki da bincike a kan zamantakewar al’umma tare da hadin gwiwar hukumar bada tallafi ta kasar Birtaniya suka shiryawa ‘yan jaridar da ke bada rahotanni daga wuraren da suke da tashe-tashen hankula.

Masana harkokin yada labarai sun kalubalanci ‘yan jarida game da rawar da ya kamata su taka a yayin gabatar da aikinsu cikin jin tsoron Allah da kuma yin taka tsan-tsan wajen kawo rahotannin da za su ruguza al’umma ba tare da ruruta wutar rikicin da ya taso ba. Ga rahoton Zainab Babaji daga Jos.

XS
SM
MD
LG