Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rayuka Fiye Da Goma Suka Salwanta A Harin Da Aka Kai Taraba


Taraba State Kidnappers
Taraba State Kidnappers

Wasu mahara sun kai hari

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar mahara sun yi dirar mikiya a garin Takum na anguwar Abakwa dake kan hanyar Wukari Road, inda suka bude wuta, kuma rayuka fiye da goma suka salwanta.

Wannan al'amarin ya farune dalilin rikicin dake tsakanin al’ummar Jukun da Tibi, da yaki karewa, lamarin da ke ci gaba da janyo asarar rayuka da dukiya.

Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz ya tuntubi shugaban riko na karamar hukumar, Mista Shiban Tikari, wanda ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce an samu asarar rayuka.

To sai dai kuma a martani, shugaban kungiyar al’ummar Tibi na Taraba Cif Dahida ya musanta zargin cewa su suka kai harin.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraban DSP David Misal, tuni aka tura karin jami’an tsaro zuwa garin Takum.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG