Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Hana Shigowa Da Motoci Ta Kan Iyakokin Najeriya


Tashar Jiragen Ruwan Najeriya Dake Apapa Lagos
Tashar Jiragen Ruwan Najeriya Dake Apapa Lagos

Hukumar Kwastam ta Najeriya tace daga ‘daya ga watan Janairun shekara mai zuwa zata hana shigowa da motoci ta kan iyakokin kasar, sai dai a rika shigowa da su ta tashoshin jiragen ruwan Najeriya

Wata sanarwa da hukumar Kwastam ta fitar da hannun kakakinta Mr. Wale Adeniyi, itace ta bayyana cewa za a fara shigo da motoci ta tashoshin jiragen ruwan Najeriya, wanda zai karawa Najeriya kudaden shiga da take samu daga ketare.

Sanarwar dai ta rawaito cewa shugaban hukumar kwastam kanal Hamid Ali mai Murabus, na cewa matakin umarni ne daga fadar gwamnatin tarayyar Najeriya.

Ambasada Muktar Gashas, daya daga cikin shugabannin kungiyar masu shigo da motoci ta Najeirya, yace wannan wani yunkurine na ganin an dawo da harkokin sayar da motoci a kasar. Amma wanne irin shiri gwamnati tayi na dawo da harkar gida? Ya kuma kara da cewa dole sai gwamnati ta gano dalilan da suka sa masu shigo da motoci suka daina shigowa ta Lagos suka koma Kwatano.

A daya bangaren kuwa masu daga cikin dillalan motocin hawa a Najeriya, sun bayyana matakin da cewa abin yabawa ne, to sai dai kuma a maimakon wannan mataki kamata yayi gwamnati ta rage kudaden fito da ta ke karba daga hannun masu shigo da motoci, al’amarin da zai sa a dawo da shigo da motoci da sauran kayayyaki ta Najeriya ba wai sai an gabatar da wannan doka ba.

Bayan matakin da gwamnatin Mohammadu Buhari ta dauka na hana shigo da motoci ta kan iyakokin Najeriya dai, a can baya gwamnatin ta dauki wasu makamantan wannan doka akan hana shigo da shinkafa, abin da ya sanya tsadar shinkafar yanzu haka a Najeriya.

Wannan mataki da gwamnatin Najeriya ta dauka zai kara kudaden shiga gwamnatin jahar Lagos, bayan ita kanta gwamnatin Najeriya.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG