Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Yi Biris Da Batun Mbappe, Ta Ci gaba Da Shirye-shiryen Karawa Da Liverpool


'Yan wasan Real Madrid suna atisaye a ranar Talata 24 ga watan Mayun 2022
'Yan wasan Real Madrid suna atisaye a ranar Talata 24 ga watan Mayun 2022

A ranar Asabar Mbappe, ya shammaci mutane bayan da ya sanar da cewa zai ci gaba da zama a kungiyar ta PSG, lamarin da bai yi wa Madrid da magoya bayanta dadi ba.

Kungiyar Real Madrid ta ki cewa uffan kan batun janyewar da Kylian Mbappe ya yi na komawa kungiyar ta Sifaniya.

Kamfanin dillancin labaran AP ya ruwaito cewa Madrid ta mayar da hankalinta kan shirye-shiryen karawarta da Liverpool a wasan karshe na UEFA Chmapions League.

Kwanaki hudu kafin karawar, rahotanni sun nuna cewa mai horar da ‘yan wasan Carlo Ancelotti da ‘yan wasansa, sun yi kokarin kaucewa yin magana kan batun Mbappe, wanda ya fasa komawa kungiyar daga PSG ta kasar Faransa.

A ranar Asabar Mbappe, ya shammaci mutane bayan da ya sanar da cewa zai ci gaba da zama a kungiyar ta PSG, lamarin da bai yi wa Madrid da magoya bayanta dadi ba.

A baya, Mbappe ya yi ta nuna sha’awar barin PSG zuwa Madrid, wacce ya ce kungiya ce da ya jima yana burin taka mata leda tun yana yaro.

Sai ga shi ya janye, duk da damar da ya samu ta komawa kungiyar.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG