Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Kada Levante Zuwa Rukunin ‘Yan Dagaji


'Yan wasan Real Madrid suna murnar lallasa Levante

Wannan nasara na zuwa ne yayin da Real Madrid take shirye-shiryen karawa a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai ta Champions League.

Kungiyar Real Madrid ta lallasa ‘yan wasan Levante da ci 6-0 a gasar cin kofin La Liga ta kasar Sifaniya.

Wannan nasara na zuwa ne yayin da Real Madrid take shirye-shiryen karawa a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai ta Champions League.

A zangón wasa na farko Ferland Mendy, Karim Benzema, Rodrygo da Vincius Jr suka ci kwallaye hudu.

Mai horar da ‘yan wasan Real Madrid Carlo Ancelotti na ta gwada dabarun da zai tunkari Liverpool a wasan karshe na Champions League.

Wannan shan kaye da Levante ta yi a hannun zakarun gasar ta La Liga, na nufin ita ce kungiya ta farko da za ta koma rukunin ‘yan dagaji (relegation) a gasar.

A gefe guda kuma, Real Sociedad ta doke Cadiz da ci 3-0, abin da ya ba ta damar da za ta kara a kakar wasa ta gaba.

Ita ma Villarreal ta samu ci gaba bayan da ta lallasa Rayo Vallecano da ci 5-1, wanda hakan zai ba ta damar karawa a gasar zakarun turai a kakar wasa ta gaba.

Wannan nasara ta ba Villarreal maki hudu da ya ba ta tazara da Athletico Club Bilbao, wacce ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Granada.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG