“Bari in gaya muku karara bin hanyoyin lallama sun kare. Muna duba sabbin hanyoyi ta hanyar diflomasiyya, tsaro da kuma matakan tattalin arziki, mun baje komai akan teburi.” In Tillerson.
A ziyararsa ta farko zuwa Asiya a wannan makon, Tillerson, tsohon shugaban kamfanin mai wanda bai da kwarewar ayyukan diflomasiyya, ya ziyarci makwabtan kasar Korea ta Arewa Japan, Korea ta Kudu da kuma China.
Sabon nadin na shugaban kasa Donald Trump na babban jami’in diflomasiyya ya sauka a barikin sojojin saman Osan ta Amurka a jiya juma’a da safe inda ya hadu da kwamandojin dakarun Amurka a Korea kafin ya ziyarci kwamandan yankin Jami’an soja mai karfi wanda ake kira (DMZ) a takaice.
Facebook Forum