Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigakafin COVID-19 Da Ake Gwaji a Amurka Na Nuna Alamun Nasara


Wani wanda ake yi wa gwajin riga kafin cutar Coronavirus.
Wani wanda ake yi wa gwajin riga kafin cutar Coronavirus.

Kwararru a Amurka sun ce wani rigakafin cutar corona da ake gwadawa na nuna alamun iya samar da kariya sosai daga cutar.

Wannan rigakafi da ake gwadawa, wani kamfanin Amurka ne mai suna Modern ya kirkiro shi sannan wasu kwararru a Cibiyar Nazarin Cututtuka Masu Yado Ta Kasa su ka dada inganta shi.

A wani rahoton da aka buga a wata mujallar magunguna mai suna New England Journal of Medicinejiya Talata, masu gwajin sun yi allura ma mutane 45 da su ka amince a yi gwajin a kansu, ‘yan shekaru 18 zuwa 55.

Kwalbar riga kafin COVID-19 da ake gwaji
Kwalbar riga kafin COVID-19 da ake gwaji

Masu gwajin sun ce babu wani daga cikin wadanda aka yi gwajin da su da ya samu wata matsala sosai sanadiyyar shan maganin, baya ga kimanin rabinsu da su ka ce sun dan ji gajiya, da dan ciwon kai, da dan sanyi sanyi haka, sai kuma dan zafi da jijiyoyinsu a daidai inda aka masu allurar.

Musabbabin gwajin na wannan mataki na farko, shi ne a san adadin maganin da ya kamata a sha, da sanin ko yana da illa ko a’a; da kuma sanin ingancinsa wajen bayar da kariya daga cutar corona.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG