Ga bisa dukkan alamu jamiyyar APC a jihar Katsina na kan hanyar fadawa cikin rikici.
Wannan kuwa ya fara fitowa fili ne biyo bayan taron da wasu ‘ya’yan ta suka gudanar a gidan Sardauna dake Kaduna.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun koka cewa anyi yaki dasu amma an barsu da kutirin bawa.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Nasir Yakubu Birnin Yero yace Alhaji Kabir Abdullahi Murja daya daga cikin masu fada aji a jamiyyar ta APC a jihar Katsina, yace yau shekaru biyu ke nan da ‘yan watanni bayan cin zabe amma talakkawa sai kuka suke yi.
Yace sun baiwa gwamnati lokaci ne ne domin kar aga gajin hakurin su, domin talakkawa zasu dauka dasu ake damawa amma an kyale su a gefe guda.
Ga Nasir Birnin Yero da karin bayani.
Facebook Forum