Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigima Tsakanin Soja Da Yan Sanda Kan Shinkafar Da Ake Rabawa Mabukata A jihar Borno


Wata hayaniya ta barke tsakanin ‘yan sandan dake tsaron gidan gwamnatin jihar Borno da wasu jami’an soja, kan Shinkafar da gwamnatin jihar ke rabawa mabukata.

Bayanai na nuna cewa an samu wannan rashin jituwar ne a lokacin da jami’an soja sukayi kokarin kutsawa inda ake rabon wannan shinkafa, a fadar gwamnatin jihar, wanda dogarawan ‘yan sandan sukayi kokarin dakatar da su.

Hakan ne ya haifar da wannan takaddama tsakaninsu har akace sojan sun harbi ‘daya daga cikin ‘yan sandan dake aikin tsaro a gidan gwamnatin jihar.

Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya ziyarci inda ake wannan hayaniya inda ya ganewa idonsa yadda jami’an ‘yan sanda sun kama wasu soja biyu aka kuma sakasu cikin wata mota domin zuwa a kulle su.

Saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG