Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Tsakanin Bangaren Zartaswa Da Majalisar Dattawa Kan Maganar Tsige Shugaba Buhari


Rahotanni sun bayyana cewa rikici dake faruwa tsakanin bangaren zartaswa dana majalisar dattawa ya bude wani sabon babi wanda ya nuna cewa magoya bayan shugaban majalisa wato Bukola Saraki sun yi barazanar tsige shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan kuwa ya biyo bayan zargin da aka yi na cewa shugaba Muhammadu Buhari nada hannu a shari’ar da shugaban majalisar Bukola Saraki ke fuskanta, kuma wanda ya fara maganar tsige shugaban kasar shine sanata Dino Melaiye.

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yammacin jiya laraba, Dino Melaiye ya bayyana cewa labarin kazon kurege ne kawai, kuma masu yada irin wannan labara makiya mulkin demokaradiyya ne. Ya kuma kara da cewa ya lashi takobin kare mulkin demokaradiyya da kasar ta kwashi lokaci mai tsawo tana morewa ko ana ha-maza ha-mata.

Akan wannan batu ne wakiliyar sashen Hausa muryar Amurka Madina Dauda ta nemi jin ta bakin sanata Suleman Nazib, daga jihar Bauchi inda ta tambaye shi cewa tunda maganar ta fito yaya yake kallon wannan batu?

Yace “mun dauki wanda yayi wannan Magana ne tamkar yana mafarki, mu ‘yan majalisu ne kuma sanatoci a karkashin jam’iyyar APC dan haka dole ne mu kare mutuncin shugabak kasa Muhammadu Buhari, da jam’iyyar mu ta APC, kuma babu wanda ya isa ya kawo wannan Magana a sai dai a mafarki, kuma muna nan muna kare masa muradunsa.”

Da tayi maganar rashin jituwa tsakanin majalisa da bangaren shugaban kasa, sanatan ya kara da cewa wannan wata Magana ce daban, domin kuwa a cewar sa kamar yadda aka sani babu abinda zai hana mayar da yawu a siyasance.

Ga cikakken rahoton Madina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG