Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ta Cafke Masu Sace Mutane Domin Kudin Fansa 11


Kama mutane goma sha daya da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi ya sake fito da nau’in masu sace mutane a yammaci da tsakiyar arewacin Najeriya inda a wani lokaci duk ‘yan arewacin kasar ne a wasu lokuta kuma gamin gambizar kabilu daban dabanne ke haduwa domin sace mutane.

Sace mataimakin jakadan Saliyo a najeriya manjo janaral Alfred Nelson, ya azzama wannan sabon bincike inda bayaga kwato jami’in diplomasiyyar, ya kaiga kama wadanda ake zargi da sace shi, harma da satar babban manajan kamfanin dangote domin neman kudin fansa.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna dai ba bakuwar hanya bace wajan yawan hadarurruka da fashi da makami duk kuwa da cewa babbar hanya ce kuma tagwaye.

Gano wadanda suka hallaka kanar Sama’ila Yunusa a jihar Kaduna daga binciken da jami’an ‘yan sanda suka gudanar ya nuna muhimmancin aiki tare tsakanin jami’an tsaron Najeriya domin gano miyagun mutane.

Satar shanu da mutane yasa rundunar sojin Najeriya ta yi rawar dajinta ta wannan shekarar a jihar zamfara domin domin kara kaimi wajan yaki da wadannan mugayen ayyuka.

Ga cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG