Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Cikin Gida A Jam’iyyar APC Reshen Jihar Yobe


APC
APC

Wutar rikici na kara ruruwa tsakanin uwar Jam’iyyar APC ta kasa da reshen Jam’iyyar a jihar Yobe. Rikici dai ya samo asali ne yayin da jam’iyyar APC reshen jihar Yobe ta kori ko dakatar da wasu jiga-jigan Jam’iyyar daga wasu kananan hukumomi guda Hudu, wanda suka hada da Fune da Fika da Potiskum da kuma Nangere bisa wasu zarge zarge.

Uwar Jam’iyyar ta kasa baki daya tace matakin jam’iyyar a jihar Yobe, ba dai dai bane kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Babban lauya Dakta Muiz Banire, wanda yake shine mashawarcin jam’iyyar APC ta kasa baki daya kan harkokin Shari’a, yace “idan ka duba kundin tsarin mulkin Jam’iyyar mu babu wani reshen jam’iyyar da ya isa ya kori ‘ya ‘yan jam’iyya, sai majalisar zartarwa ta kasa baki daya..” ya ci gaba da cewa idan akwai wani mataki ba wanda ya fada to shiriri ta ne.

Sai dai kuma jam’iyyar APC a jihar Yobe, tace bata gamsu da matsayin uwar jam’iyyar ta kasa ba, a cewar shugaban jam’iyyar na jihar Alhaji Adamu Chillare, yace mai baiwa jam’iyya shawara kan harkokin Shari’a bai isa yace ya mayar da hukuncin da suka yanke a jiha. Alhaji Adamu yace idan har wasika bata fito daga ofishin shugaban Jam’iyya na kasa ba to bazasu canja hukuncin su ba.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG