Accessibility links

Jam'iyyar APC a jihar Sokoto ta fada cikin rikicin bangaranci sanadiyyar shiga Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko cikin jam'iyyar.

Kokuwar iko tsakanin gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko da ya shiga jam'iyyar adawa ta APC kwanan nan da tsohon gwamna Attahiru Bafarawa da aka kafa jam'iyyar a jihar da shi ta fara kawo bangaranci a jam'iyyar ta APC a Sokoto.

Wannan rigimar ta kai ga kiran taron manema labarai da bangaren Bafarawa ya kira inda ya nuna rashin amincewarsa da abin da ya kira shigar takama da kuma babakeren da gwamna Wamakko da mukarrabansa ke niyyar yi. Wannan taron ya kuma biyo bayan cewa da gwamna Wamakko ya yi zai sa a nada shugabannin jam'iyyar daga mataki na kasa har zuwa karshe a jihar don karfafa ta, abinda bangaren Bafarawa ke fassarawa da cewa neman yin babakere ne.

Mai magana da yawun bangaren na Bafarawa a wurin taron Hakibu Dalhatu ya ce sam ba za su amince da hanyar da gwamna Wamakko ya shigo jam'iyyar ba. Ya ce muddun gwamnan bai shiga jam'iyyar ta hanyar da ta dace ba to jam'iyyar za ta tagayyara. Malam Hakibu ya kuma amsa cewa lallai jam'iyyar ta kasu zuwa bangarori biyu a Sokoto.

To amma Shugaban Dandalin Shugabannin Majalisun Mulkin Kananan Hukumomin jihar Sokoto, kuma Shugaban Majalisar Mulkin Karamar Hukumar Sabon Birni Alhaji Idris Mohammed Gobir ya ce bai kamata wani ya nuna wata damuwa ba saboda wasu sun shiga jam'iyyarsa. To saidai Alhaji Idris ya jaddada cewa kamar yadda abin ya ke a ko'ina a kasar, gwamnan jiha ne shugaban jam'iyya a jiharsa. Don haka shi ya kamata ya gina jam'iyya.

XS
SM
MD
LG