Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Habasha Ya Tilasta Yiwa Gwamnatin Kasar Garambawul


Firayim Ministan Habasha Hailemariam Desalegn

Karshenta dai, Firayim Ministan Ethiopia Hailemariam Desalegn ya bada sanarwar yiwa gwamnatinsa garanbawul biyo bayan tashe tsahen hankula da aka share wattani ana gudanarwa, wanda ya kai gwamnati kafa dokar ta baci.

Duka-duka dai Majalisar kasar ta Habasha ta amince da sabbin ministoci 21 ne da aka zabo a jiya Talata.

Wasu ministoci tara a cikinsu sun ci gaba da rike tsofaffin ma’aikatunsu a wannan garanbawul din.

Zanga zangar kin jinin gwamnati, wadda ta faro a kan batun fili daga bisani ta bazu zuwa lardunan Oromia da Amhara. Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Right Watch tace sama da mutane 500 suka mutu a arangama tsakanin fararen hula da yan sanda da sauran jami’an tsaro.

Yanzu dai masu zanga zangar sun karkatar da akalarsu ne zuwa ga lamuran hakkin bil Adma da mulki, musamman da yake ana ganin kamar ‘yan kabilar Tigrayan ne suka mamaye jami’iya mai mulkin kasar.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG